Yadda Ake Magance Matsalar Shan Mb ( Data ) A Wayar Android Cikin Sauki – Kabasto.Com


Yadda Ake Magance Matsalar Shan Mb ( Data ) A Wayar Android Cikin Sauki.

Barkanku da zuwa wannan website namu mai albarbar wato Gidanhausatv. com Bisa la’akari da ƙorafe-korafen mutane game da matsalar shan MB (Data) muka ga ya dace mu kawo muku hanyar da za ku bi wajen magance wannan matsala ta shan MB/Data.

 

Akwai abubuwa da dama da suke kowa wannan matsala ta shan MB/Data a wayar Android, manyan daga cikin su sun haɗa da Google Play store, saukar da application mai bude kansa wanda ke amfani da yanar gizo, ko kuma yakan iya zama updating da wasu application keyi na kansu muddin sun shunshuni yanar gizo.

 

Koma daga ina matsalar take ga hanyoyi da zaku bi wajen magance wannan matsalar. Abun kula nan shine ko wace waya tana da hanyar shan data amma dai kashi casa’in bisa dari suna faruwa ne bisa hanyoyi dana ambata a baya ga kuma yanda za,a magance matsalar.

 

 

Cikaken hanyoyi da zaka bi wajen wagance shanyewar data, mb ko megabyte a wayar salulanka na android.

 

Mataki na Farko

Dakatar da Application daga Updating kansa: akwai application da dama wanda akowani karshen wata ana da’da musu abubuwa sabbi a ciki wanda kafin mutum ya samu damar aiki da wannan sabin ababen dole sai yayi updating na application dinsa. Sai a wasu lokutan Muddin wayar android ya sami data a bude baya tambayar mutum ko yana bukatar sabon update sai dai kawai ya saukar masa a cikin wayar sa na salula wanda hakan ke janyo karewar data.

 

Dan magance wannan matsalar akwai hanyoyi da dama wanda mutuum zai iya bi amma mafi sauki daga cikin hanyoyin shine dakatar da updating application daga settings na Google Play store, dan dakatarwa sai mutuum ya shiga Google Play store Application >> sai yaje zuwa ga ‘settings’>> sai ya zabi “Auto Update Apps” sannan mutum sai ya kuma zabi na farko wanda aka rubuta “Do not auto-update apps” ma’ana kar yayi updating wani application. Wannan shine hanya mafi sauki wajen magance application da ke updating kansa.

 

Mataki na Biyu,

Dakatar da Google Play store daga aiki ko kuma Application masu aiki in sun sami data a bude: Google play store gidane da babban kamfanin nan na google ke kula dashi wanda ke baiwa mutane damar saukar da application a wayar salulansu, saukar da application a waya dai yana cin yan wasu mb.

 

Duk lokacin da wannan application din yake aiki ko yana bude akwai wasu yan chargi da ake ma mutuum haka zalika ba lallai sai mutuum ya bude da hannunsa ba yakan iya fara aiki da kansa wanda hakan ke janyo karewar data ko mb a wayar salulan mutum.

 

Dan dakatar da Google play store na wayar ka sai ka ziyarci ‘settings’ na wayarka >> sannan sai aje izuwa ga >> ‘Application’ ko ‘Apps’ ya dangana da yanda yake rubuce a wayar>> sannan sai mutum ya zabi “All apps” ko kuma mutuum ya zabi “All application” to anan mutum sai ya nemi>> “Google Play Store” a jerin application da suke wayar bayan mutum ya samu sai ya shiga akwai akwa tuna biyu wanda aka tanadar sai a latsa na biyun wanda ke dauke da “Force Stop” ma’ana dakata daga aiki> zai tambayeka shin ka tabbatar kana son Dakar da wannan application din sai ka zabi ‘Ok’ ma’ana eh. Shikennan anan an magance matsalar shan data ko mb wanda google play store keyi.

 

Za,a iya bin hanya daya gabata wajen magance shanyewar data da wasu application keyi amma lokacin da mutuum yazo zaban application mai makon ya zabi “Google Play store” sai ya zabi application da yake tunanin yana yawan bude kansa.

 

Mataki na karshe

Dakatar da sync settings na wayar salulanka: dan dakatar da syn settings na wayar salula ga mata kan kamar haka kaje izuwa ga “Settings” Ka dan tafi can kasa, sai ka zabi “Account and sync settings” Ka cire zabin da ke kan “Background data”. Ka maida shi babu zabi, zasu yi maka gargadi, kawai ka manta da su, ka cire alamar zabi.

Duba Cigaban A nan ƙasa : Yadda Ake Magance Matsalar Shan Mb ( Data ) A Wayar Android Cikin Sauki.

Allah Ya taimaka.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *