Yadda Ake Magance Matsalar Shan Mb ( Data ) A Wayar Android Cikin Sauki  – Kabasto.Com

Yadda Ake Magance Matsalar Shan Mb ( Data ) A Wayar Android Cikin Sauki  – Kabasto.Com


Yadda Ake Magance Matsalar Shan Mb ( Data ) A Wayar Android Cikin Sauki

Barkanku da wannan lokaci, sannunku da sake kasancewa da wannan website namu mai albarka Kabasto.Com

Akwai dalilai da yawa da suke jawo ‘data’ take ƙarewa da wuri a waya.

Na farko, amfani da social media irinsu Instagram, Tiktok, Youtube, da Facebook Reels… saboda streaming.

Sannan na biyu, tara tarkacen ‘apps’ a waya. Kusan kowanne app dake wayarka, yana amfani da data, wani kaɗan, wani da yawa.

Na uku, barin wayarka tana ‘updating’ ko yi ma ‘backup’ ko ‘downloading’ na files kai-tsaye (automatic). Shi ma na jan data gwargwadon aikin da ta ma.

1. Ka maida wayarka ‘data save mode’. Wannan tsari zai kange sauran ‘apps’ daga amfani da datarka (background data), sai iya wanda ka buɗe, kake amfani da shi a lokacin.

Kowacce waya tana da wannan tsari, in ka shiga ‘Phone Setting’ > ‘Network and Internet’; zaka riske shi a can insha Allah.

2. Ka rage yawan ‘apps’ na wayarka. Wani lokacin muna tara ‘apps’ barkatai a waya.

Misali, a cikin ‘apps’ 10 in ka tattare su, sai ka ga guda biyun ko ɗaya ciki kaɗai, za su iya wadatar da kai.

• Babu amfanin ka haɗa Chrome, Firefox, Opera… a waya a daya. Browser ɗaya ta wadatar.

• Babu amfanin ka haɗa VLC, HD Video Player, QQ Player a waya ɗaya. Player ɗaya ta wadatar.

• Babu amfanin ka haɗa Gmail, Yahoo Mail, Outlook, Email App a waya ɗaya. Zaka iya ɗora kowanne irin mail a Gmail, shi kaɗai ya wadatar.

 

Amma muna tara ‘apps’ da yawa, suna zuƙe mana data, suna shanye mana caji, suna sa wayoyinmu ɗaukar zafi da nauyi.

 

3. Ka rufe ‘auto-downloading’ ma cikin Whatsapp da Telegram. Ka rufe ‘video auto-play’ a Facebook. Ka rufe ‘auto-backup’ a Photos. Kusan duk mai iya karanta rubutun nan a yanzu, akwai wannan a wayarsa.

 

4. Idan baka sa data mai yawa, ka rage shiga Instagram, Tiktok, Youtube ko buɗe Reels a Facebook. A kasa da 1 hour, za su iya zuƙe ma 1GB ko fiye.

 

5. In baka sa data mai yawa a wayarka, ka koma amfani ‘Lite App’, Facebook Lite, Instagram Lite, Twitter Lite… ba sa jan data kamar ‘normal app’.

 

Allah Ya yi jagora.

Comments

No comments yet. Why don’t you start the discussion?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *