Hukumar Bada Agaji Ta UNICEF Za Ta Dauki Ma’aikata -Health & Nutrition Officer
Hukumar ba da agajin gaggawa ta UNICEF ta fara ɗaukar ma’aikata ɓangaren Health & Nutrition Officer
Barkanku da wannan lokaci, sannunku da sake kasancewa da wannan website namu mai albarka Kabasto.Com
UNICEF wato ‘United Nations International Children’s Emergency Fund’ Da farko ana ƙiranta da Asusun Ba da Agajin Gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya gaba ɗaya, wanda yanzu ya zama asusun kula da yara na Majalisar ɗinkin duniya.
UNICEF Wata hukuma ce ta Majalisar ɗinkin duniya da ke da alhakin ba da agajin jin kai da ci gaban yara ga yara a duniya.
Hukumar dai na daga cikin ƙungiyoyin jin daɗin jama’a, hukumar ta yaɗu a duniya kuma ta samu karɓuwa da ƙaunar al’ummar duniya bisa taimakon rayuwar al’umma da take.
Hukumar ta UNICEF tana rassa 192 a sassan duniya. Ayyukan UNICEF sun haɗa da samar da alluran rigakafi, da rigakafin cututtuka, ba da magunguna ga yara da iyaye mata masu fama da cutar kanjamau, inganta yara da kuma abinci mai gina jiki na mata, inganta tsafta, inganta ilimi, da bayar da agajin gaggawa domin tunkarar bala’o’i.
A yanzu haka wannan hukuma ta UNICEF za ta ɗauki ma’aikata a sassa da dama, kuma kamar yadda kuka sani ba wannan koronta na farko ba, hukumar ta saba ɗaukar al’umma a sassan duniya aiki kuma tana biyansu kuɗi mai kauri duk wata.
Mai sha’awar cike wannan aiki a hukumar bada agajin gaggawa ta UNICEF ya shiga rubutun da ke nan ƙasa domin ya yi apply👇
Allah Ya yi jagora